Ban Fahimci Dalilin da Ya Sa Aka Kayar da APC A Edo -El-Rufai

Ra’ayoyin jama’a sun nuna APC za ta ci zaben Edo, ban san me ya faru ba -El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce yana da kyakkyawan fata har zuwa makonni uku da suka gabata cewa jam’iyyarsa, All Progressives Congress, ce za ta lashe zaben Gwamnan Jihar Edo

Ya ce kuri’un jin ra’ayin da aka gudanar sun nuna cewa dan takarar jam’iyyar APC, Osagie Ize-Iyamu, ne zai lashe zaben, yana mai cewa bai san abin da ya faru ba a cikin makonni uku da suka gabata na yakin neman zaben.

Da yake tsokaci game da ci gaban, gwamnan jihar Kaduna, wanda ya yi magana a safiyar ranar Litinin yayin da yake bayani a gidan Talabijin na Channels, ya ce zaben “mai kyau ne”.

“Makonni uku da suka gabata, zaben ya nuna karara cewa APC za ta yi nasara amma sakamakon ya fito daban da abin da muke tsammani.

“Obaseki ya ci nasara, shi ke nan. Ba zai yiyu a shiga zabe ba tare da yiwuwar faduwa ba. ”

Ya kara da cewa, “zaben ya kasance mai inganci. Duk da cewa mun damu da tashin hankalun da suka faru a yayin zaben amman dai abubuwan sunyi sauki sosai da sosai.”
Gwamnan ya kuma jaddada cewa gwamnatin Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta himmatu wajen gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Obaseki murnar lashe zaben sa jim kadan bayan INEC ta sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More