Ban taba shan kaya ba – kwamishinan yansandan Kano

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Mohammed Wakili, wanda aka fi sani da sunan ‘Maza Kwaya-Mata Kwaya’, ya karyata jita jitan dake yawo cewa, shi dan kwaya ne, yana mai cewa, bai taba shan kwaya ba a rayuwarsa.

Da yake tattauanawa da ‘yan jarida, Mista Wakili ya ce, haka Allah ya hallice shi, “Yanayin da nake da yadda nake magana ya kan sa mutane su dauka ni dan kwaya ne. “Watakila saboda yadda nake harkoki na, gare su hakan yana nuna kamar ni dan kwaya ne, kuma mutane kan yi dariya a kan yadda nake magana tare da amfani da hannaye na, wannan kuma haka Allah ya hallice ni.

“Haka Allah ya hallice ni kuma babu abin da zan iya yi akai, ban taba shan kwaya ba a dukkan rayuwana, har zuwa lokacin da na shiga aikin dan sanda, kuma kafin ma in shiga aikin dan sanda ban taba sanin sunayen wadanna kwayoyin ba gaba daya,” inji shi. Mista Wakili ya kuma jaddada matsayinsa na ci gaba da yaki da shan miyagun kwayoyi, yana kuma mai cewa, ina dan kokari na ne a kan kawar da shan miyagin kwayoyi a cikin al’umma saboda na san irin barnar da take yi a cikin al’umma.

“Ba zan iya zura ido ba tare da na bayar da nawa gudumawar ba a kan yadda za a yi maganin wannan matsalar da a take fuskantar, wannan kuma ya yi daidai da matsayin dana samu kai na ne. “Ina tsammanin sanin irin barnar da kwayoyin nan suke yi a tsakanin al’umma ya sanya na kara dagewa don ganin bayan shan miyagun kwayoyi a cikin al’umma, kuma sanin illar shan miyagun a cikin al’ummar mu ya taimaka mani kwarai da gaske wajen fuskantar wannan aiki dana sa gaba.”

“In dukkan jami’an tsaro suka hada hanun don yaki da wannan mugun halin to lallai za mu iya maganin shan kwayoyin da ake tafkawa a cikin garuruwanmu.” Daga nan sai Mista Wakili, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki musamman hukumomi irinsu NDLEA da NAFDAC da sauransu, da su tabbatar da ci gaba da aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata don samun wannnan nasara. “Malaman addini da Sarakunan garhajiya za su iya taimaka matuka don kuwa idan sun yi magana jama’ar su na saurarawa saboda haka suna da mahimmanci a yakin da ake yi da shan miyagun kwayoyi da bangar siyasa da kuma sauran miyagun ayyuka,” inji Mista Wakili.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More