Barawo ne dan sandan da zai karbi kudin beli – Kwamishina

Kwamishinan yan sandan jahar Legas, Zubairu Mu’azu ya ce  duk yan  sandan da ke karbar kudin beli sun fi masu garkuwa da mutane domin  kuwa bashi da bambaci da barayin mutane,karbar kudin fansa  abu ne mai muni.

Kwamishinan ya fadi hakan ne a ranar Talata a garin Legas yayin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da dakin rubuta shaida a sashen binciken masu aikata manyan Laifuka (SCIID) a Panti.

Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma ja kunnen jami’ansa da su guji karbar cin hanci daga hannun mutanen da suka kama saboda hakan yana bata wa rundunar suna a idon duniya baki daya.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More