Barcelona na da sha’awar dawo da Neymar

Dan kasar Brazil din ka iya komawa tsohuwar kungiyarsa a karshen kakar wasa ta bana.

Kamar yadda rahotanni daga kasar Spain ke nuni, Neymar ya gana da jami’an Barcelona a watan da ya gabata don tatraunawa kan yiwuwar komawarsa Camp Nou.

Gidan radiyon Catalunya ya yi ikrarin cewa dan wasan mai shekaru 26 ya tattauna da jami’in kungiyar dan kasar Brazil Andre Cury a birnin Paris kafin kirsimeti, inda kungiyar ta nuna sha’awarta na ganin yarjejeniyar dawo da dan wasan ta tabbata.

Rahotanni sun kuma ce dan wasan gaban ya yi dana-sanin sauya sheka zuwa PSG kuma ya kagu da ya koma tsohuwar kungiyarsa a karshen kakar wasa ta bana.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More