Barcelona ta dauki Kevin-Prince Boateng daga Saussuolo

Kungiyar ta Blaugrana ta ba da sanarwar daukar tsohon dan wasan na AC Milan, wanda ke fatan buga wasan Elclasico na nan gaba.

Zakarun gasar na Laliga na da zabin daukar dan wasan mai shekaru 31daga Saussuolo kan kudi fam miliyan £7.1 a karshen kakar wasa ta bana.

Boateng ya je Tottenham daga Hertha Berlin a 2007, amma bai dade ba aka bayar da shi aro zuwa Dortmund, sannan zuwa Postmouth.

Tsohon dan wasan kasar Ghana haifaffen kasar Jamus, ya shafe tsawon kakar wasa biyu a AC Milan, sannan ya koma Schalke, Las Palmas da Frankfurt.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More