Barcelona za ta kece raini tsakaninta da Manchester United a gasar Zakarun Turai 

A ranar Laraba ne Barcelona za ta ziyarci Old Trafford, domin buga
wasa da Manchester United a gasar Zakarun Turai ta Champions
League.
United za ta karbi bakuncin kungiyar ta Spaniya a wasan daf da na
kusa da na karshe a gasar ta Zakarun Turai ta Champions League.
Tuni kocin Barcelona, Ernesto Valverde ya bayyana ‘yan wasa 22 da
zai je da su Ingila ranar Talata, domin buga karawar zagayen farko.

Kungiyoyin biyu sun fafata a gasar Zakarun Turai sau 11, inda
Barcelona ta ci wasa hudu, United ta yi nasara a karawa uku da
canjaras hudu.
‘Yan Barcelona 22 da aka bayyana:
Ter Stegen da Semedo da Pique da Rakitic da Sergio da Todibo da
Coutinho da Arthur da Suarez da kuma Messi.
Sauran sun hada da Dembele da Malcom da Lenglet da Murillo da
Jordi Alba da Prince da Roberto da Vidal da Umtit da Alena da kuma
Inaki Pena.
Sakamakon wasa hudu da suka kara a bayan nan:
Champions League 28 ga watan Mayu 2011
Barcelona 3 – 1 Man Utd
Champions League 27 ga watan Mayu 2009
Barcelona 2 – 0 Man Utd
Champions League 29 ga watan Afirilu 2008
Man Utd 1 – 0 Barcelona
Champions League 23 ga watan Afirilu 2008
Barcelona 0 – 0 Man Utd
Barcelona ta lashe kofin Champions League guda biyar, yayin da
Manchester United take da shi guda uku.
Sai dai United tana ta shida a kan teburin Premier da maki 61, ita
kuwa Barcelona tana ta daya a teburin La Liga da tazarar maki 11
tsakaninta da Atletico Madrid ta biyu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More