Bashi BilIyan 110 Sabon Gwamnan Gombe ya tarar

Bayan rantsar da sabon Gwamnan Jahar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, a matsayin gwamnan Jahar na hudu a jiya Laraba 29 ga watan Mayu 2019 a filin wasa na Pantami Township Stadium, da ke Gombe.

 

Gwamna Inuwa Yahaya, ya shelanta dakatar da duk wasu nade-naden da tsohuwar gwamnatin da ta gabace shi ta yi daga ranar 10 ga watan Maris, 2019 har zuwa lokacin.

 

Sabon gwamnan ya kuma ce, zai kuma duba sahihanci da kuma kishin cibiyoyin gwamnatin da tsohuwar gwamnatin ta Ibrahim Dankwambo ta kafa su, bayan ya yi nazari a kan dimbin basukan da suka kai Naira bilyan 110 da tsohuwar gwamnatin ta tara masa.

Ya yi alkawarin magance yanda lamarin ma’aikatan Jahar ya tabarbare, ta hanyar yin duba a kan abin da ya karin girma da sauran hakkokin ma’aikatan Jahar.

 

Inda ya umarci dukkanin Sakatarorin kananan hukumomin Jahar guda 11 da su karbi ragamar gudanar da harkokin kananan hukumomin daga hannun shugabannin kananan hukumomin a take, har zuwa lokacin da za a nada wasu shugabannin riko na kananan hukumomin ko kuma a gudanar da zabe, Sai tsohon gwamnan  jahar Dankwambo  bai halarci taron rantsarwar ba.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More