Batun taba Ka’aba: Abunda Daurawa ya fada

Hukumomi a Saudiyya sun wallafa wasu ka’idojin kariya daga cutar Coronavirus  ga mahajjatan da aka yarjewa sauke farali a bana.

Sabbin ka’idojin sun hada da haramta wa mahajjata taba Ka’aba yayin aikin Hajjin wanda ake ganin ya shafi hana taba Hajraul Aswad da ake taɓawa lokacin ɗawafi.

A hirar da BBC ta yi da fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Daurawa,  ya bayyana abubuwan da ake yi wa Ka’aba guda biyu ne dama, akwai zagayeta da kuma taba  Dutsen Hajar al-Aswad da Rukn al-Yamani.

Wadannan wurare biyu an sunnanta taba su ko sumbata, sannan a inda Hajar al-Aswad ya ke ana son mutum ya sumbace shi ko ya taɓa da hannu ko sujada ko kuma a yi amfani da sanda wurin nuna shi, in ji Daurawa.

”Idan kuma aka samu akasi na cunkosa ko wani dalili tun da wuri ne da mutane ke burin tabawa sosai, sai a yi amfani da dan ‘yatsa a nuna shi.”

Sheikh Daurawa ya ce ”babu wanda ya ce taba ka’aba wajibi ne a musulunci bayan wandanan wurare guda biyu da kuma Multazzam wato daidai kofar ka’aba.

”Multazzam kuma wuri ne da ake son idan mutum zai yi addu’a ya rungumi wurin ya fada wa Ubangiji bukatunsa.”

A cewar Sheikth Daurawa, dukkan wadanan wurare guda uku babu wanda ya zamo cikin rukunan aikin Hajji ko farilar hajji, kawai dai yana cikin sunnoni, idan ka yi zaka samu lada.

”Saboda cunkoson ganin yadda milyoyin mutane ke zuwa hajji da zagaye ka’aba aka baka damar cewa idan akwai cunkosa ko cutuwa to ka nuna shi daga nesa ka ce Allahu Akbar.

”Kowa na da dama guda biyu idan baka iya taba ko wadanne wannan wurare ba to ka nuna su dan ‘yatsa ka yi kabbara ka wuce.”

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More