Bayanin Fadar Shugaban Kasa Kan Abinda Yashafi Dakatar Da Twiiter a Najeriya

Dakatar da Tiwita na dan wani lokaci ba anyi haka bane kawai don martani kan cire wallafa maganar Shugaban kasa, akwai Matsaloli da iri iri da suka jima dangane da kafafun sada zumunta na zamani a Najeriya, a anan ne ake janyo Mumunar fahimta da yada Labaru na kanzon kurege, wanda a gaskiya ya janyo tashin hankalin Duniya. Tun tsawon lokaci, kamfanin ta gaza sauke hakkin doka a kanta.
Duk da haka, Cire maganar shugaba Buhari a Tiwita abin takaici ne, Idan akan yi duba kalubalen halayyar rashin fahimtar da ƙasar Najeriya ke fuskanta a yau.
Cikin jawabin da Shugaban Kasa yayi a Zauren Babban dakin Babban taron Majalisar Dinkin Duniya a 2019 wanda yace “Duniya ta kadu da Firgita game da daukan rayukan mutane 50 masu Ibada da wani dauke da bindaga yayi a Ƙasar New Zealand.”
Wannan da Miyagun aiyuka irin sa wanda Kafofin sada zumunci ba zama ya janyo yana bazuwa da kunno kai zuwa har sau 28 ga masana’anta da Al’adar Na’urar Zamani.
Dole kamfanin Sadarwa na Major Tech’ su tashi su tsaya kan hakkokin samar dasu. Ba mai yiwuwa bane a barsu kara zube ake amfani dasu Gurin yada Banbancin Addini, Nuna wariyar launin fata, Nuna Ƙyamar baki, da sakonni na karya wanda zasu iya tunzura Al’umma baki daya kan Saura, wanda kan janyo rasa rayuka da dama. Akan iya raba kan wasu kasashe.
A saboda haka Shugaban kasa yayi gargadi kan shishshigi ba kafafen Sada zumunta da tsoma kawo rabuwa da Matakan da Gwamnati ta dauka kan cire bayanin Shugaban kasa ba wai anyi ne haka siddan batare da nazari kan shi ba, sabanin tunanin abinda sakon ke dauke dashi wanda ya zamo wajibi a karanta gaba daya.
Sakon Shugaban ba barazana bace, face gaskiyar maga.
Ƙungiyar Ta’addanci ta IPOB ta jefa barazana ga zama lafiya da tsaron Al’umman Najeriya.
Lokacin da Shugaban yace za’a bi dasu ta “ta Yaren da suke fahimta,” karara ya kara jaddada cewa karfin su zai hadu da wani karfi. Wanda kuma wannan wani manuface da martani na aikin tsaro da ake amfani dashi a duniya baki daya.
Wannan ba kalman tunzura nuna tsana bane, sai dai yin Alkawari na kiyaye Ƴancin Ƴan kasa daga Cutaswa. Bazai yiwu a tsammaci Gwamnati ta zamo mai yin saranda ga Ƴan ta’adda ba.
Ƙungiyar IPOB haramtacciya ce karkashin Dokar Najeriya, Membobinta ta kashe Ƴan Nijeriya da basuji ba basu gani ba. Sun kashe Ƴan sanda da cin na wuta kan kadarorin Gwamnati. Yanzu sun tattara Gurin kera gwajin makamai da Boma bomai a Fadin Kasar nan.
Kafar Tiwita bataga irin halin Ha’u la’i da yakin basasa ya jefa Kasar ba. Wannan Gwamnati bazata taba bari irin wannan bala’i ya faru

 

CC: Buhari Sallau

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More