Bayyanan kwakwaso kan zaben Jahar Kano

Tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya ce zaben gwamna da za a kammala a jihar Kano zai tabbatar ko kuma rushe darajar gwamnati da hukumar zabe ma zaman kanta ta kasar Najeriya wato INEC.

 Jahar Kano na daga cikin jahohi biyar da hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta ce za ta gudanar da zaben a ranar 23 ga watan Maris.

Wannan mataki ya zo ne bayan da hukumar zabe mai zaman kanta  wato INEC ta ce zabukan jahohin ba su kammala ba saboda soke sakamakon wasu mazabu, wadanda yawan kuri’unsu suka zarce tazarar da ke tsakanin ‘yan takara biyu mafiya yawan kuri’u a zaben na gwamna.

A tattaunawar sa da BBC gabanin zaben, Sanata Kwankwaso ya ce zaben na jahar Kano na daukan hankulan al’ummar Najeriya da ma wadansu kasashe.

Ya kara da cewa ‘wannan shi zai tabbatar da darajar ita kanta hukumar zabe da gwamnati, ko kuma ya ruguje ta.’

A zaben gwamna da aka gudanar na jahar Kano, ranar 9 ga watan Maris, jam’iyyar PDP ce ke kan gaba da yawan kuri’a, inda ta samu kuri’u 1,014,343, sai jam’iyyar APC mai mulkin jahar wadda ta samu kuri’a 987,829.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More