Baza’a rantsar da Diri na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan Bayelsa ba – Oshiomhole

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Kwamrad Adams Oshiomhole ya bayyana cewa, babu wanda zai rantsar da dan takarar Jam’iyyar PDP wato Sanata Douye Diri, a matsayin gwamnan jahar Bayelsa a gobe ranar Juma’a 14 ga watan Fabrairu 2020.

Oshiomhole ya bayyana cewa hukuncin kotun kolin na cewa, a bada sabuwar takardar shaidar cin zabe ga dan takarar da yake da abubuwan da aka bukata a zaben baya ga David Lyon, inda yace Diri bai cike bukatun kotun kolin ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More