Bazan sake yiwa shugaba Buhari waka ba sai duk talakan Najeriya ya bani naira 1000 – Dauda Kahuta Rarara

Fitaccen mawakin siyasa nan na Hausa Dauda Kahuta Rarara, wanda ya yi fice wajen yi wa Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari na Najeriya waka, ya bayyana cewar, ba zai sake yi masa waka ba sai an hada masa kudin yin wakar.

Rarara ya shaida wa BBC cewa zai sake yi wa Shugaba Buhari waka ne kawai idan talakawan da suka zabe shi kowannensu ya mika masa naira 1000 ta hanyar saka masa a wani assun bankinsa.

“Talakawa masoya Buhari na ainihi wadanda kuma akwai su, su ne za su ba ni naira dubu dai-dai sannan zan yi wa Buhari waka,” in ji mawakin.

Ya ce ya yanke shawarar hakan ne sakamakon yadda ake yada jita-jita a shafukan sada zumunta cewa Shugaba Buhari ya gaza a mulkinsa shi ya sa ya ce ba zai sake yin waka don talakawa su ji dadi ba sai sun biya kudi.

Dauda Rarara ya kara da cewa har yanzu yana goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More