Bazan yi kuskuren neman mulkin kasa Najeriya karo na uku ba – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba shi da sha’awar kara mulkin Najeriya a matsayin shugaban kasa da sunan neman wa’adin mulki na karo uku.

Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC wanda aka gudanar a yau  Juma’a 22 ga watan Nuwamba 2019 hedikwatar  jam’iyyar APC ta kasa dake babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban Buhari ya karyata rade radin da wasu yan siyasa ke yin na cewa zai neman zarcewa da wa’adin mulki karo na  uku kamar yadda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fada. Inda wasu ke zargin Buhari na shirin ne da hadin bakin yan majalisu.

A jawabinsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar ma mahalarta taron cewa zai tattara inasa inasa ya bar fadar gwamnatin Najeriya zuwa shekarar 2023 a karshen wa’adin mulkinsa na biyu saboda kundin tsarin mulkin Najeriya ya haramta neman wa’adin mulkin na uku.

Buhari ya yi kira ga shuwagabannin jam’iyyar APC dasu mayar da hankali a mazabunsu, tare da tabbatar da sun mamaye mazabunsu a siyasance ta yadda zasu zama masu fada a ji domin kuwa, abun kunya ne a ce APC ta rushe bayan karewar wa’adin mulkinsa.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More