#Bidiyo: Jawabin Shugaba Buhari a mabarin majalisar dinkin duniya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sake gabatar da muhimmiyar bukata ta magance matsalar kafewa da tafkin Chadi ke ci gaba da fuskanta a sanadiyar sauyin yanayi.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a wajen taron majalisar Dinkin Duniya karo na 74 a tarihi da ya hallarta, inda ya ce tsukewar da tafkin Chadi ke yi illa ce ga mutanen da suka dogara da shi wajen noma da sana’ar su. Sannan ya  jaddada bukatar hadin kan sauran shugabannin kasashen duniya domin magance wannan barazana da ta tunkaro al’ummomin da suka dogara a kan tafkin.

Shugaba Buhari yace hafbaka zaman lafiya a kasashen duniya baki daya da kuma kare hakkin dan adam tare da muhalli domin tabatar da zaman lafiya da samar wa al’umma abunda zasu amfani shi.

Haka kazalika kuma ya kara da cewa Najeriya za ta ci gaba da hadin kai da sauran kasashen duniya da manufar dawo da martabar tafkin domin inganta rayuwar jama’ar da ke kewaye da shi gami da samar da tsaro. Inda yayi magana kan iftili’in da ya afku na kwanikin da suka wuce na kin jinin baki.

 

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More