#Bidiyo:Kotu ta bada umarni a bawa Dasuki fasfo dinsa

Wata babbar kotu dake babban birnin tarayyar  Abuja karkashin shugabancin Alkali  Hussein Baba Yusuf, ta ba da umarnin a baiwa tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki ritaya, fasfo dinsa.

Alkalin  yayi umarnin hakkan ne bayan da lauyan Dasuki yayi jayayyar takardar da aka shiga  na 11 ga watan Fabrairu.

Tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a lokacin mulkin  dakta Goodluck Jonathan ya bukaci a bashi fasfo dinsa  ne da ya samu dama sabunta shi, duba da gama aiki da fasfo din yayi, wanda ke kotun har tsawun shekaru biyar.

Ana tuhumar Sambo Dasuki ne kan zargin mallakar makamai a gidansa, da kuma na halatta kudaden haram.

Hakkan ne yasa  aka kwace fasfo din na sa a kan sharadin bayar da belinsa.

Kotun ta  dage zaman sauraran  shari’ar ta Sambo Dasuki  zuwa  ranar 13 ga watan Maris 2020.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More