Bidiyon cin hanci: Kuto ta dakatar da binciken Ganduje

Wata babbar kotun jahar Kano da ke Najeriya ta dakatar da majalisar dokokin jahar daga binciken da take yi a kan zargin da ake yi wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje na karbar hanci.

Majalisar dokokin ta kaddamar da kwamitin domin bincike kan bidiyon da ya nuna Gwamna Ganduje yana karbar miliyoyin dala daga wurin wasu ‘yan kwangila wanyanda ba’a san su waye.

Sai dai  kotun ta bukaci kwamitin ya dakatar da binciken zuwa wani lokaci da za ta saurari karar da wata kungiyar lauyoyi ta gabatar mata.

Shugaban kungiyar Barrister Zubairu Muhammad ya yi zargin cewa majalisar dokokin jahar Kano ba ta da hurumin gudanar da bincike a kan Gwamna Ganduje kasancewar yana da rigar-kariya.

A cewar kungiyar, binciken da kwamitin ke yi tamkar cin zarafin kundin tsarin mulkin Najeriya ne.

 

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Comment moderation is enabled. Your comment may take some time to appear.