#Bidiyo:Zargin Zamba: Ba A Tura Wa Shehu Sani Kudi A Asusun Banki Sa Ba – Shaidun EFCC

An cigaba da zaman kotun a yau 26 ga watan fabrairu dan sauraran karar da EFCC ta shigar na kalubalantar tsohon dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu sani bisa zargin zamba cikin aminci na dala 25,000, wanda kotun ta bayar da belinsa.

Shaidu EFCC biyu ne suka bayyana a gaban kotun a yau, mai’aikacin bankin Zenith mai suna Remijus Ojo da kuma dan kasuwa( canjin kudi), mai suna Abukakar Ahmed.

Miss Ojo ya bayyana wa kotun cewa, a ranar 20 ga watan Nuwamba 2019 ne Abubakar Ahmed ya tura naira miliyan biyar (5m) zuwa asusun bankin ASD.

Abubakar Ahmed Shaida na biyu ya tabbatar da mu’amalar kudaden asusun bankin, inda ya bayyana wa kotun cewa, ASD ya bashi takardar cheque na dala 13,930 wanda ya canja zuwa naira miliyan biyar (5m) sannan ya tura asusun bankin Alhaji Sani Dauda na kamfanin motocin ASD daga bankin sa na Zenith.

Yayin da akayi wa shaidun tambaya a kotun, wanda ke cewa, ko sun san wanda ake tuhuma?

Mita Ojo ya amsa da cewa, baisan wanda ake tuhumar ba , yayin da Ahmed shima yace basan shi ido-ido ba amma yana ganin sa a kafar yada labarai.

A karshe kotun karkashin shugabancin Alkali Inyang Ekwota ta dage zaman zuwa 4 ga watan Mayu 2020 dan cigaban sauraron karar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More