Bikin diyar shugaba Buhari: Mai zanen barkunci bai yi wa yata adalci ba – Aisha Buhari

Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta ce zanen barkwancin da Mustapha Bulama ya yi da ke nuna yadda take nuna wa ƴan Najeriya hotunan bikin yarta Hanan Buhari su kuma yan ƙasa na nutsewa a cikin kogi saboda wahala ‘”babu adalci a ciki”.

Mai magana da yawun Aisha, Aliyu Abdullahi ya shaida wa BBC cewa ƴaƴan kowanne shugaba na da damar aure idan lokaci ya zo ko da yan kasa na jin daɗin mulkinsu ko akasin haka.

Zanen barkwancin Mustapha Bulama da ke yawo babu adalci a ciki saboda bikin ba shi da wata alaƙa da yanayin da yan kasa suka tsinci kansu, kuma saboda irin haka ne ya sa wata guda kafin bikin, shugabar tawa ta tattauna da ma’aikatanta cewa ba ta son a yayata bikin saboda za a taƙaita hidima.”

“Hoton da shugaba ta (Aisha Buhari) ta wallafa na ma’auratan a soshiyal midiya na bayan biki ne domin ta gode wa wadanda suka aike da fatan alheri da kuma sanar da ƴan kasa.

”Ina iya tabbatar muku cewa bikin Hanan Buhari shi ne wanda kwata-kwata babu armashi kuma aka taƙaita idan aka kwatanta da bukukuwan baya da aka yi a kasar nan.”

Kakakin nata ya kuma ce bidiyon da aka rinka yadawa da ke nuna yadda mutane ke yi wa ma’auratan liƙi ɓangaren dangin ango ne bayan an kai musu amarya.

“Wannan bidiyon da ke nuna mutane na liƙi da kudin naira ba a Abuja ba ne a gidan surukan Amarya ne bayan ta isa gidan dangin mijin a Kaduna,” a cewar kakakin uwargidan Buhari.

Aliyu ya kuma ce uwargidan shugaban kasa ta damu da annobar cutar coronavirus da dokokin da likitoci suka gindaya da masana kimiyya, kuma ta tabbatar da hidimar da ta shirya mutane sun bi wadannan dokoki.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More