Biyayya ga umarnin kuto ne zai sa mu saki Sowore – Malami

Gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi alkawarin sakin matashin dan siyasar nan kuma dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore, kamar yadda wata babbar kotun tarayya ta bukata.

Rahoton gidan rediyon BBC ta ruwaito ministan Shari’a kuma babban lauyan Najeriya Abubakar Malami ne ya bayyana haka cikin wata hira da ya yi da gidan rediyon, inda yace gwamnati za ta yi biyayya ga umarnin kotu wajen sakin Sowore wanda ya kwashe kwanaki fiye da 50 a hannu.

Wannan hukunci ya biyo bayan janye bukatar cigaba da rike Sowore da hukumar DSS ta yi ne a gaban kotun, amma dai kotun ta sanya sharadin samun beli daga DSS ga Sowore, inda ta umarceshi ya ajiye fasfonsa na tafiye tafiye.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More