Boko Haram: Akwai bukatar shugaba Buhari yasan jami’an tsaro na yin  zagon kasa a yunkurin murkushi kungiyar  _ Babagana Zulum

Gwamnan jahar Borno, Babagana Umara Zulum ya sake nanata cewa kokarin murkushe kungiyar Boko Haram na shan zagon kasa daga wani rukuni na jami’an tsaron kasar ta Najeriya.

Gwamna Zulum ya bayyana cewa,  ba zai iya yin shiru cikin yanayi na kashe-kashe ba, saboda rantsuwar da ya yi tsakaninsa da Allah a kan zai kare al’ummar jaharsa.

Wannan na zuwa ne yayin da jahar Borno ke samun  karuwar hare-haren ‘yan ta-da-jayar-baya.

Ko a ranar Asabar sai da wani hari ya kashe mutum 15 ciki har da kananan yara a yankin kan iyaka cikin kasar Kamaru.

Gwamnan dai ya ce akwai bukatar shugaba Muhammadu Buhari ya san cewa zagon kasan da ake yi daga cikin harkar tafi da tsaro na kawo cikas ga kokarin kawo karshen rikicin ‘yan ta-da-kayar-bayan na sama da shekaru goma.

BBC ta rawaito cewa, Babagana Zulum na jawabi ne gatse-gatse kwanaki kalilan bayan kwambar motocinsa mai matukar tsaro kwatsam ta yanke tafiya, kuma ya juya ya tsere daga garin Baga na kusa da Tafkin Chadi saboda barin wutar bindigogi babu kakkautawa.

Sai dai Sojoji sun dora alhakin abin da ya faru kan Boko Haram, inda Zulum ya nuna cewa da hannunsu a  cikin abin da ya faru, wanda har ya sake yin  amfani da kalmar “zagon kasa”.

Wata sanarwa da aka wallafa a shafukan sada zumuntar gwamnan ta ambato shi yana fadawa takwarorinsa gwamnonin APC yayin wata ziyarar jaje ranar Lahadi cewa:
“Zan ci gaba da yin tsayuwar daka, daram kan kudurin cewa Allah ne kadai ke ba da mulki.

Ba na neman wa’adi na biyu, idan ya nufe ni da kammala wannan ma, to na gode Allah. Amma ni a matsayina na gwamna, na yi shiru al’umma jahar Borno miliyan shida su mutu, su kare, hakan ba zai zama alheri gare ni ba.

Na yi rantsuwa tsakanina da Allah zan kasance mai gaskiya ga al’ummata,” in ji Gwamna Zulum

Ya kuma tuhumi abin da ya sa sojojin Najeriya suka hana dubban mutanen da rikicin ya raba da gidajensu koma wa gonakinsu a lokacin da su sojoji ke noma a filaye.

Sai dai BBC ta tuntubi rundunar sojin Najeriya don jin martaninta game da wadannan manyan zarge-zarge, amma ta ce ba ta sa-in-sa da shugabannin siyasa

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More