Bollywood: ‘Yan Sanda Sun Gayyaci jaruma Deepika Padukone Kan Binciken Miyagun Kwayoyi

An gayyaci fitacciyar jarumar Bollywood Deepika Padukone don yi mata tambayoyi a wani bangare na binciken miyagun kwayoyi da ake game da kisan dan fim Sushant Singh Rajput.

An kama ’yar fim Rhea Chakraborty da ake zargin ta da siyawa tsohon saurayinta Rajput kwayoyi maye, wanda aka tsinci gawarsa a watan Yuni a gidansa da ke Mumbai – ’Yan sanda sun tabbatar da cewa Sushant ya kashe kansa ne.

Deepika Padukone jaruma wacce take da fina-finai da dama da suka yi fice zuwa yanzu, mutuwar jarumin dan shekaru 34 da farko ya haifar da muhawara kan lafiyar kwakwalwa a masana’antar Bollywood.
Amma danginsa sun ki yarda game da rahotannin da ke cewa ya kamu da ciwon kwakwalwa haka zalika sun zargi Chakraborty, mai shekara 28, da satar kudaden sa da musguna masa. amman Chakraborty ta musanta zargin hakan.
Babbar hukumar da ke yaki da aikata manyan laifuka a Indiya, ta fara binciken mutuwarsa tun a watan jiya. Ofishin Kula da Miyagun Kwayoyi (NCB) suna duba yadda yake amfani da miyagun kwayoyi.

A farkon wannan makon, tashar TVN TimesNow ta watsa sassan hirar ta WhatsApp yadda yan masana’antar ke amfani da miyagun kwayoyi duk da suna zargin cewa mutanen biyu da suke tattaunawa Padukone ne da manajan ta.

KP.S. Malhotra, Mataimakin Darakta na Hukumar ta NCB, ya fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa hukumar za ta kirawo Padukone da kuma ‘yar fim din Sara Ali Khan, Shraddha Kapoor da Rakul Preet Singh don amsa tambayoyi.

Tuni ‘yan sanda suka tsare wasu da suke da danganta da lamarin ciki har da dan uwan ​​Chakraborty da kuma wani ma’aikacin gidan Rajput.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More