Bugun zuciya ne ya kashe shugaban Burundi Pierre Nkurunziza

Wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ranar Talata ta ce Shugaban Burundi, Pierre Nkurunziza ya rasu ne sakamakon bugun zuciya, ya rasu yana da shekaru 55.

Sanarwar ta kara da cewa ranar Asabar da daddare aka kwantar da Mr Nkurunziza a wani asibiti mai suna Karusi bayan ya dawo daga wasan kwallon kafa a kusa da gidansa.

Gwamnatin kasar ta sanar da zaman makokin kwana bakwai daga ranar Talata.

Mr Nkurunziza ya jagoranci Burundi tun daga 2005 kuma yana shirin mika mulki ga zababben shugaban kasar, Evariste NDayishimiye a ranar 20 ga watan Agusta.

A shekarar 2015, sanarwar da ya bayar cewa zai tsaya takara a karo na uku ta jefa kasar cikin tashin hankalin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More