Buhari bai rarraba kawunan ‘yan Najeriya ba – Adesina

Menene ra’ayinku game da wannan batu?

Fadar shugaban kasar Najeriya ta maida martani kan wasu manyan jami’an gwamnatin da ake ikirarin  cewa, ta kara rarraba kawunan ‘yan Najeriya.

Mai ba shugaba Muhammadu Buhari shawarwari kan harkokin sadarwa da hulda da jama’a Femi Adesina, ya musanta zargin hakkan a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Channels a ranar Laraba.

Da yake maida martani kan kalaman tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, da kuma na fitaccen marubucin Najeriya wanda ya sami lambar yabo ta Nobel  wato Farfesa Wole Soyinka, wadanda suka bayyana takaicin rarrabuwar kawuna da tsatsaguwa da ake ci gaba da samu a kasar da suka ce, ta kara ta’azzara karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

Adeshina yace, idan za a yi la’akari da kalaman tsohon shugaban kasar da kuma na Farfesa Shoyinka a lukutan baya, za a fahimci cewa, an dade da samun rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yan Najeriya.

 Femi Adeshina ya kuma  bayyana cewa, babu wani lokaci a tarihin Najeriya da kasar ta ke hade tun daga shekara ta dubu dari tara da goma sha hudu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More