Buhari na nuna banbanci – wasu yan Najeriya

Yan Najeriya da dama sun cec kuce tare da yin suka  kan alhinin Shugaba kasar Muhammadu Buhari da ya nuna na mutuwar wani mutum a Legas, yayin da suke zargin shugaban da cewa ya yi buris da halin da mutanen  jahar Zamfara ke ciki na kashe da ta’addancin da ake yi a kusan kowace rana.

Shugaban Buhari dai ya jajanta wa iyalai da abokan arzikin Mista Kolade Yusuf wanda ake zargin ‘yan sanda ne suka kashe a Jahar Legas.

A wani sako da fadar shugaban kasar ta wallafa a Twitter ranar Litinin, ta bayyana cewa wadanda ake zargi da kisan an kama su kuma suna fuskantar tuhuma kan lamarin.

Sai dai wannan sakon jajen na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rahotanni na kisan gilla da ‘yan fashi ke yi a Zamfara da kuma wasu sassa a Najeriya, tare kuma da sace mutane don neman kudin fansa a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Bayan da fadar shugaban kasa ta wallafa wannan sako a shafinta naTwitter, jama’a da dama sun ta kawo suka tare da yin zargin cewa shugaba Buhari yana nuna bambanci.

Akasarinsu sun bayyana cewa an yi kashe-kashe a Zamfara da wasu wurare amma shugaban bai jajanta ba ko da a shafukan sada zumunta ne.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More