Buhari Ya Bada Umarnin Bincike Kan Kashe Jimoh Isiaq da ‘Yan Sanda suka Yi A Oyo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan kisan da ‘yan sanda suka yi wa Jimoh Isiaq Ogbomosho, a jihar Oyo. Shugaban ya fadi haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin karfafawa matasa gwiwa na shugaban kasa a babban birnin tarayya yayin da yake jawabi ga matasan Najeriya da ke zanga-zangar nuna rashin adalci da kashe-kashen da ‘yan sanda ke yi wa ‘yan Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari Ya kuma yi alkawarin tabbatar da cewa za a gudanar da bincike don hukunta jami’ai, wadanda suka aikata ba daidai ba. Ya ce, “Za mu kuma tabbatar da cewa an gurfanar da duk wadanda ke da halin rashin da’a ko aikata ba daidai ba a gaban shari’a. “Mun kuma yi matukar nadamar asarar rayukan da aka yi a Jihar Oyo yayin zanga- zangar kwanan nan.
“Na bayar da umarnin cewa ya kamata a binciki yanayin mutuwarsa sosai.”

Shugaban ya cewa bai kamata a bar wasu ‘yan tsirarun balagurbin yan sanda su bata sunan hukumar ‘ yan sanda ba.
An kashe Isiaq lokacin da ‘yan sanda suka bude wuta a kan masu zanga-zangar a Zanga-zangar kira da a soke shahen hukumar yan sanda da ke yaki da fashi da makami ta (SARS),wacce aka faro daga ranar Laraba, ta bazu zuwa sassa daban-daban na kasar, duk da cewa an samu biyan bukatun farko na zanga-zangar, wanda shi ne na soke sashin rundunar ‘yan sanda na musamman masu yaki da fashi da makami, masu zanga-zangar suna yanzu suna neman a yiwa rundunar ‘yan sandan Najeriya garambawul.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More