Buhari ya bukaci amincewar majalisa dan karbar bashi

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi Majalisar Tarayya ta sake dubawa tare da sahhale kudirin neman bashin da ya aika wa majalisa ta takwas mai suna 2016-2018 External Borrowing Plan.

Shugaban ya gabatar da bukatar hakkan ne a wata wasika da ya aike wa yan majalisar kuma aka karanta ta a yau Alhamis 28 ga watan Nuwamba 2019 a zauren majalisar.

Buhari ya bayyana a cikin wasikar cewa za a karbo bashin $29.96 don aiwatar da manyan aiyukan more rayuwa wanda alummar  dake fadin kasa ta Najeriya  zata amfana biki daya.

Ya kuma yi bayanin cewa majalisa ta takwas, karkashin jagorancin Abubakar Bukola Saraki, wani bangare kawai na dokar ta amince da shi, “abin da ya kawo tsaiko ga wasu daga cikin ayyukan raya kasar da gwamnatinsa ke yi,” in ji Buhari.

Shugaban ya ce ayyukan da rashin amincewa da kudirin ya shafasun hada da hakar ma’adanai da wutar lantarki da lafiya da noma da ruwan sha da kuma ilimi.

“Saboda haka na hado maku da kwafin bayanai daga Ministar Kudi da Tsare-Tsare game da ayyukan da muke bukatar gudanarwa idan kuka amince da kudirin 2016 – 2018 External Borrowing.”

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More