Buhari ya ji tsoron daga hannun dan takara a Zamfara

Rikicin ‘yan takarar jam’iyyar APC a Zamfara ya hana shugaba Muhammadu Buhari daga hannun dan takarar gwamna a jihar.

A yayin yakin neman zabensa a Zamfara a ranar Lahadi, Buhari ya ce “duk gardamar da ake idan abu yana wurin shari’a za mu dakata.”

Hakan dai ya kara tabbatar da cewa APC a Zamfara na cike da rudani bayan shugaban ya kasa daga hannun ‘yan takara.

Hukumar zaben kasar INEC ta kara jaddada wa BBC matsayinta cewa APC ba ta da ‘yan takara a zaben 2019 a Zamfara.

Kafin jawabin Buhari, gwamnan jihar mai barin gado Abdulaziz Yari Abubakar ya ce ba za su tilasta wa shugaban daga hannun ‘yan takara ba kamar sauran jihohi.

“Ba za mu tilasta ma sa yin abin da yake da shakku ba.”

“Idan mun tilasta ka cewa sai ka daga hannayen ‘yan takara to muna ganin ba mu yi maka adalci ba saboda kasashen duniya za su kalubalanci matakin domin za a tilasta ka yin wani abin da kotu ba ta bada izinin a yi ba.” In ji shi.

Gwamnan ya ce da yardar Allah da ‘yan takarar APC za a yi zaben 2019.

Tun da farko, a wani gangamin siyasa gwamna Yari ya yi barazanar cewa zabe ba zai yiyu ba idan har babu ‘yan takarar APC.

Ya ce bisa ga hukuncin da kotun Gusau ta zartar, INEC ba ta da hurumin hana wa ‘yan takarar APC shiga zabe, inda ya ce kotun ta yi umurni ga INEC ta karbi ‘yan takarar jam’iyyar.

A cikin jawabinsa a Zamfara, shugaba Buhari ya ce yana fatan kafin ranar Asabar, hukumar zabe za ta fito ta fadi dan takarar da ta yadda da shi.

Sai dai kuma Buhari ya yi kira ga mutane su fito su zabi wanda suke so, a gaban gwamnan Zamfara da ke gawagwarmayar tabbatar da kwamishinansa na kudi a matsayin gwamna.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More