Buhari ya rage yawan tafi-tafiyen shugabannin ma’aikatu.

Shin kuna kanin hakan zai yi tasiri?

Shugaban kasa Najeriya Muhammadu Buhari ya rage yawan tafiya-tafiyen shugabannin ma’aikatu Najeriya, da hukumomin tarayya zuwa kasashen waje. Yayin da gwamnatin ke kokarin gyara-gyare da rage yawan kashe kudi da taka-tsantsan da baitul malin gwamnatin tarayya.

Inda sanarwa da jaridar Vanguard ta ruwaito ta bayyana cewa,daga yanzu ana bukatar manyan jami’an hukumomi su gabatar da jadawalin ziyarar su zuwa ga ofishin sakataren gwamnatin tarayya a farkon shekara.

Inda sai fadar shugaban kasa ta amince da duk wani tafiya,  da gwamnati zata dauki nauyin sa da takardu, ya zama dole a rage tawagar minista da za su yi wani tafiya zuwa kasar wajen dan yin hutu.

Shugaba Buhari ya yi umurnin takaita tafiya-tafiyen zuwa 2 a kowani zango na shugabannin hukumomi, a ranar Laraba 16 ga watan Oktoba 2019.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More