Buhari ya taya Ganduje da Lalong murnar lashe zabe

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya taya gwamnan jahar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da gwamnan  jahar Filato Simon Lalong, murnar samun nasara a kotun sauraron korafin zabe.

Kotunan sauraron korafin zaben gwamna a Kano da Filato, sun tabbatar wa da gwamnonin na APC nasarar da suka samu a zaben da aka gudanar cikin watan  Maris 2019.

A sanarwar kakakin shugaban kasa Malam Garba Shehu ya fitar da cewar, Buhari ya bayyana nasarar da gwamnoni suka samu a matsayin nasara ga dimokradiyya.

Gwamnonin biyu na daga gwamnoni uku da suka raka shugaba Buhari zuwa kasar Afrika ta kudu, shugaban kasar ya taya su murna ne a filin jirgi na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja jim kadan kafin su tashi zuwa kasar Afrika ta kudu.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More