Buhari ya tsege Baffa Bichi shugaban TETFund daga mukaminsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya cire shugaban Asusun kula da karatun gaba da sakandare da bayar da tallafin karo karatu, wanda aka fi sani da TETFund Dr  Abdullahi Baffa Bichi.

A sanarwar da wani jami’in yada labarai na ma’aikatar ilimi Mr Bem Goong  fitar na bayyana  cewa an maye gurbin Dr Bichi da Farfesa Suleiman Bogoro, wanda a baya ya taba zaman shugaban asusun.

Sai bubu wani dalili  da ya bayyan sanadiyar   tsege  Dr Bichi daga kan mukaminsa ba, amma daga cikin  wasu masu sharhi sun na ganin  cewa an cire shi ne dalilin tsunduma cikin harkokin siyasar Jahar Kano maimakon mayar da hankali a kan aikinsa.

Wasu mukarraban gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na ganin Dr Bichi na da hannu a rura wutar da ta taso lokacin da aka zargi Gwamna Ganduje da karbar cin hanci a wasu bidiyon da suka nuna karbar dala daga hannun wanda ba’a san ko su waye ba.

A shekarar 2016 ne Dr Bichi ya maye gurbin Farfesa Bogoro a matsayin shugaban TetFund bayan an sauke Bogoron daga kan mukamin.

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne ya nada Farfesa Bogoro kan mukamin a 2014.

Yanzu dai za a iya cewa hannun bayar wa ne ya mika wa hannun karba.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More