Buhari ya zake kawo kujerar Najeriya

Bayan kammala tattaro alkalumma daga jihohi 36 da Abuja, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya sake lashe kujerar shugabancin kasar a karo na biyu.

Tun kafin a kai karshen bayyana sakamakon zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya yi wa abokin takararsa, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP fintinkau.

Duk da kuwa Atikun ya lashe wasu jihohi, ciki har da jihohin Arewa, amma wannan bai ba shi damar yin kafada da kafada da Buhari a jihohin Arewa ba.

Shugaba Buhari ya lakadawa Atiku duka a jihohin Arewa irinsu Zamfara, Kebbi, Sakkwato, Yobe, Borno, Kano, Kaduna, Katsina da sauransu.

Wanda saboda tsabar yawan kuri’un da ke tsakaninsu, dole ta sa mafi yawan magoya bayan jam’iyyar APC tuni sun fara mika wuya. Babbar nasarar da Buhari ya samu a kan Atiku ita ce a Jihar Kano, inda Shugaba Buhari na jam’iyyar APC ya samu kuri’u miliyan daya da dubu dari hudu da sittin da hudu, da dari bakwai da sittin da takwas. Yayin da abokin hamayyarsa Atikun PDP kuma ya samu kuri’a dubu dari uku da casa’in da daya, da dari tara da casa’in da uku. Wannan rubdugu da Buharin APC ya yi wa Atikun PDP ya fara yin ‘yar manuniya ga sakamakon zaben Shugaban Kasan na Najeriya. Wanda tun bayan bayyanar sakamakon Tumbin Giwa gwiwowi suka sare, jikkunan ‘yan PDP suka yi la’asar da batun nasara.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More