Buhari yayi ganawar sirri da manyan rundunar tsaro

Talata 19 ga watan Maris Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron Kungiyoyi na Shugabannin rundunonin tsaro na Kasar nan.

Taron na sirri da ya dauki tsahon awonni uku ana yin sa, an gudanar da shi ne a dakin taro a fadar Shugaban Kasa Najeriya dake cikin  Billa.

Sufeton ‘yan sanda na Kasa Mohammed Adamu, shi ne ya sanar da manema labarai bayan su gama  zaman da aka yi na tattaunawar.

Wayanda suka hallarce taron sun hada  da babban Hafsan tsaron, Janar Gabriel Olonisakin, da Shugaban rundunar sojojin kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai; Shugaban Rundunar Sojojin Ruwa, Riya Admiral Ibok Ekwe Ibas, sai Shugaban Rundunar Sojojin  Sama, Iya Mashal Abubakar Sadibue.

Sauran sun hada da Darakta Janar bagaren  sashen Hukumar tsaro ta (DSS), Magaji Yusuf Bichi, da mai ba wa Shugaba Buhari shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno.

Sai Sakataren Gwamnatin Tarayya wato  Mista Boss Mustapha, da Ministan tsaro Birgediya- Janar Mansur Dan- Ali, da kuma Daraktan Hukumar tattara bayanan sirri na kasa, sai Malam Ahmed Abubakar.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More