Buhari zai kaddamar da titin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan

Ministan Sufuri, Mista Rotimi Amaechi ya ce Shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da aikin layin dogo daga Legas zuwa Ibadan a watan Janairun 2021 don inganta zirga-zirgar jigilar kayayyaki da fasinjoji a kasar.

Amaechi ya bayyana haka ne yayin ziyarar gani da ido daga Legas zuwa
Ibadan don duba yadda ake ci gaba da aikin a Ibadan ranar Asabar.

Ya ce, ‘yan kwangilar sun yi iya kokarinsu game da aikin, yayin da yake danganta yanayi a matsayin daya daga cikin kalubalen da’ yan kwangilar ke fuskanta.

“Mun sami haɗin kai daga al’ummomi daban-daban tare da aikin shimfida layin dogon,yan kwangila sunyi abinda zasu iya amma matsalar ita ce canjin yanayi.

“Ba za su iya aiki fiye da wancan lokacin ba, banda wannan, ina ganin‘ yan kwangilar sun yi rawar gani.

“An kusa kammala aikin, suna kokarin kammala aikin kafin cikar wa’adin da suka baiwa ma’aikatar sufuri,saboda akwai cigaba sosai.”Inji ministan.

#OakTVHausa#OakTVOnline

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More