Buhari zaiyi tafiya zuwa kasar Mali

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi Bamako babban birnin kasar Mali a ranar Alhamis.

Tafiyar ta shugaban kasar ta biyo bayan tattaunawarsa da Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wanda yana daga cikin masu shiga tsakani daga ƙunigyar ECOWAS da suka je Mali domin kawo sasanci.

Wasu daga cikin shugabannin kasashen Yammacin Afrika irin su Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou sun amince su hadu a Mali domin tattaunawa domin kawo sasanci tsakanin Shugaban Mali Boubacar Keita da kuma ‘yan adawa a ƙasar.

Ana sa ran Shugaban Ghana Nana Akufo Addo da kuma na Cote d’Ivoire Alassane Ouattara za su halarci tattaunawar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More