CAN ta nemi Buhari ya soke dokar CAMA

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya wato CAN ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya soke dokar CAMA wadda ya saka wa hannu ranar 7 ga watan Agusta.

Dokar mai suna Companies and Allied Matters Act (CAMA) 2020, ta tanadi cewa shugaban hukumar kula da kuma bai wa kamfanoni lasisi ta Corporate Affairs Commission (CAC) zai karbe ragamar duk wata kungiyar addini idan har aka tabbatar akwai rashin gaskiya a shugabancin kungiyar.

Kazalika dokar ta bai wa CAC ikon dakatar da kwamitin amintattun ƙungiyar addini sannan ta naɗa shugabannin riƙo idan ta aminta cewa ba a gudanar da ayyukan ƙungiyar yadda suka dace ko kuma akwai almundahana.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, shugaban kungiyar yana bayyana matsayinsu a cikin wata wasika da ya aike wa mai bai wa Buhari shawara kan Majalisar Dattawa ranar Talata

Kungiyar ta hakikance cewa ba a tuntuɓi waɗanda ya abin ya shafa ba kafin amincewa da dokar.

“Muna kallon wannan doka a matsayin wani kundi mai cike da batutuwan da za su kawo tarnaki ga tsaro da jin dadin Najeriya,” CAN ta bayyana a wasikar, kamar yadda BBC ta rawaito.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More