Ce-ce-ku-ce kan kalaman Buhari kan satar kuri’a

Al’ummar  Najeriya na ci gaba da yin tsokaci a kan gargadin da shugaban kasar ya yi cewa wanda yayi yunkurin satar akwatin da ake zuba kuri’u to yayi a bakin ransa.

Tuni dai babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta soki wadannan kalaman na shugaban kasar a cikin wata sanarwa da ta fitar.

PDP ta ce tana fatan wannan kiran da shugaban ya yi ba wata makarkashiya ba ce ta bai wa wadanda ta kira sojojin bogi da jam’iyyar ta tattara damar harbe ‘yan Najeriya su kuma dauke  akwatunan zabe su yi aringizon kuri’u a ranar zaben.

Abdullahi Umar, wani dan Najeriya ne da ke cewa shi a ra’ayinsa tun da Najeriya kasa ce da dokoki ya kamata a bi doka wajen yanke hukunci a kan kowanne irin laifi.

Abdullahi ya ce yin karan tsaye da tsallake abin da kundin tsarin mulki ya tanadar ka iya jefa rayukan ‘yan kasa cikin hadari kasancewa ba a taru an zama daya ba.

Shi ma ana sa ra’ayin Ahmed Usman, ya ce wannan ra’ayi ne irin na shugaban kasa domin akwai hanyoyi da dama da za a iya bi wajen dakile satar kuri’a ba sai ta hanyar harbi ko barazana ga rai ba.

Sai dai kwamitin kamfe na Shugaba Buhari a ta bakin Honourable Faruk Adamu Aliyu, ya ce an yi wa kalaman shugaban mummunar fahimta.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More