Chelsea na zawarcin Benzima

Bafarenshen dan wasan ka iya daure kayansa ya nufi birnin Landan don maye gurbin Morata.

Chelsea na da sha’awar daukar dan wasan gaban na Real Madrid Karim Benzema, a cewar jaridar Mirror.

Dan wasan mai shekaru 31 ya jefa wa Madrid kwallaye 7 cikin wasanni 18 ga ya buga a gasar Laliga a wannan kakar wasan, sai dai kuma ana ta rade-radin komawarsa Stamford Bridge.

Blues din na fatan maye gurbin Alvaro Morata, wanda alamu ke nuna cewa har yanzu ba tabbas din ci gaba da zamansa a kungiyar duk da kwallaye biyun da ya ci wa kingiyar a karawa da Nottingham Forest a gasar kofin FA, kuma ana danganta dan wasan na kasar Spain da komawa Sevilla.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More