Cire tallafin man fetur: Ana Jiran Hukuncin Fadar Shugaban Kasa Kan Fara Siyar Da Mai N380 Zuwa N408.5.

Cire tallafin man fetur: NNPC na jiran sakamakon taron Gwamnatin Tarayya da kungiyar kwadago a yau

Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) ba zai dakatar da tallafin man fetur ba , duk da Shawarwarin da Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta bayar kwanan nan cewa a cire tallafin.

Maimakon haka, kamfanin mai yana jiran sakamakon taron na yau (Talata) tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyar kwadago kan ko za a dakatar da tallafin kayan.

Kamfanin NNPC ne kadai ke shigo da man fetur zuwa Najeriya kuma ya ci gaba da rike wannan matsayin sama da shekaru uku, kuma ya kasance yana bayar da tallafi ga farashin kayan.

Wani kwamiti da kungiyar gwamnonin Najeriya ta kafa a ranar Laraba da ta gabata ya ba da shawarar a mayar da farashin litar mai tsakanin N380 zuwa N408.5. Kwamitin ya kuma yi kira da a hanzarta cire tallafin mai.

Mataimakin Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya, Joe Ajaero, ya fada wa manema labarai cewa kungiyar kwadago za ta gana da Gwamnatin Tarayya a yau (Talata) kan batutuwan da suka shafi farashin mai da korar ma’aikata a Kaduna, da sauransu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More