Coronavirus a Kano: Mutum na farko daya fara kamuwa da cutar ya warke

Mutum na farko da ya fara kamuwa da cutar Coronavirus a jahar Kano, Ambassada Kabiru Rabiu ya warke  daga cutar, yayin da ka sallami shi  daga wajen da gwamnatin Kano ta tanada dan killace masu cutar tare da basu kulawa da ta dace.

Majiyar ta tabbatar mana da cewa  an sake gudanar da gwajin cutar a kansa har sau biyu, ida sakamakon gwajin ya nuna cewa baya dauke da kwayar cutar, wanda yanzu haka yana cikin iyalan sa kuma cikin koshin lafiya.
A yanzu haka dai mutane 602 ne wanda ma’aikatar lafiya ta jahar Kano ta tabbatar sun kamu ta cutar Covid19.
An sallami mutane 50 wayanda suka warke daga cutar, yayin da mutane 26 suka riga mu gidan gaskiya.

Gwamnatin jahar Kano ta sanar da bullar Coronavirus a jahar a ranar 11 ga watan Aprilu 2020, bayan tabbatar da Sakomakon gwajin na Ambasada Kabiru Rabi’u ya nuna cewar yana dauke da kwayar cutar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More