Coronavirus a Najeriya: Sabbin matakan hawa jirgin sama

Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya fitar da sanarwar a shafinsa twitter, wanda ke cewa, a yau ranar Laraba 8 ga watan Yuli ne za a fara zirga-zirgar jiragen sama na cikin gida a Najeriya.

Hadi Sirika ya ce za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama daga Abuja babban birnin kasar zuwa Legas daga ranar Laraba 8 ga watan Yulin da muke ciki, Kano, Fatakwal, Owerri da Maiduguri za su koma aiki daga ranar 11 ga watan Yulin.

Sauran filayen jiragen sama kuma za a bude su don fara jigilar fasinjoji daga ranar 15 ga watan Yuli.

Inda ya kara da cewa, fasinjoji masu fita kasashen waje zasu dan dakata, domin kawu zuwa yanzu ba’a tsayar da ranar da jiragen zasu fara jigila zuwa kasahen na waje ba.

“Daga yanzu, ba za a bar dukkan manyan mutane su je filin jiragen sama da wadanda ba matafiya ba ne. Mun fadi hakan ne musamman ga gwamnoni da ministoci, da ‘yan majalisun dokokin tarayya, da alkalai da kuma sojoji.

A wani sako da ma’aikatar zirga-zirgar jirage sama ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter ta ambato Minista Hadi Sirika ya ce an dauki matakin ne domin dakile yaduwar cutar Coronavirus ga mutanen da ke dandazon zuwa filayen jiagen na sama.

Ya kara da cewa matafiya kawai za a bari su shiga filayen jiagen sama.

Ga dai jerin dokokin da hukumar kula da filayen jiragen sama na kasar ta fitar.
👇

*Dole fasinjoji su sanya takunkumi kafin su shiga filin jirgi

*A wajen shiga jirgi, kamfanonin jiragen za su diga man kashe kwayoyin cuta a hannun kowane fasinja kafin su shiga jirgi

*Bayan shinge, duk inda fasinjoji za su je, da ya hada da wajen tantancewa ko kuma wajen jira kafin shiga jirgi, akwai alamu da za su nuna yadda tsarin zaman zai kasance

*Za a saka shinge mai shara-shara a wajen da kamfanonin jirage suke tantance mutane domin kariya

*Hukumomin filin jirgi za su zana alama a kasa domin nunawa fasinjoji wajen tsayawa yayin da suke bin layin shiga filin jirgi

*Ku wanke hannunku sannan ku yi amfani da man kashe kwayoyin cuta a kai a kai

*Hukumomi za su ringa gwada zafin jikin fasinjoji

*Ba za a bar masu rakiya da suke zuwa da manyan mutane su shiga dakin jira kafin tashin jirgi ba, fasinjoji ne kawai za su shiga

*Ana shawartar masu daukar fasinjoji su ci gaba da zama a motocinsu har sai fasnjojin sun fito waje

*Ana shawartar fasinjoji su je filin jirgi sa’a uku gabanin tashin jirgi saboda sabbin matakan kariya daga kamuwa da cutar Coronavirus

*Ana fatan fasinjoji za su kiyaye ka’idar nisantar juna yayin da suke shiga motar da za ta kai su wajen shiga jirgi

*Guji taba abubuwa a filin jirgi ba gaira ba dalili

*Ba za a bar mutanen da ba tafiya za su yi su shiga gining tantance mataifya ba
Bayar da tazarar kafa shida (2m) tsakaninka da sauran fasinjoji a koyaushe.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More