Coronavirus: Abunda sassaucin dokar hana fita a Kaduna ta kunsa bayan shafe kwanakin 75 cikin kulle a jahar

Gwamnatin Jahar Kaduna ta sassauta dokar hana fita da ta saka a jahar wadda al’ummar suka kalla a matsayin mafi tsauri a arewacin kasar ta Najeriya.

Gwamna Nasir Ahmed El-Rufai ne ya sanar da hakan a wani jawabi da ya yi ga jahar ranar Talata, inda ya ce a karon farko cikin makonni masu yawa za a bar masallatai su yi sallar Juma’a sannan majami’u su gudanar da ibada ranar Lahadi.

Gwamnan ya kuma sassauta dokar hana zirga-zirga a jahar, sai dai babu fita daga karfe 8:00 na dare zuwa 5:00 na asuba kuma sassaucin zai fara aiki daga yau Laraba 10 ga watan Yuni 2020.
Sannan lokotan aiki za su rika farawa daga 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana.

Gwamna El-Rufai ya kara da cewa bisa ka’idojin da gwamnati ta shimfiɗa, wuraren sana’a za su iya budewa sannan su samar da na’urar auna zafin jikin mutum, masallatai zasu bude ranar Juma’a kaiwa, domin gudanar da ibada sai Coci-coci suma ranar Lahadi.

Sai dai gwamnan ya ce ba za a bude kasuwanni ba tukunna.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More