
Coronavirus: Adadin mutane 44,337 ne suka warke daga cutar a kasar Najeriya
An samun karin sabbin mutane 132 da suka kamu da cutar ta Covid19 a kasar Najeriya, wanda hakkan ne ya bada jumullar 56,388 da ke dauke da kwayar cutar.
Sabbin wayanda suka kamun sune:
Lagos-52
Gombe-27
Plateau-17
Kwara-10
Enugu-9
Ogun-9
Katsina-3
Ekiti-2
Bauchi-1
Osun-1
Rivers-1
An sallami mutane 44,337 da suka warke daga cutar, inda hukumar NCDC ta tabbatar da mutuwar mutane 1,083 daga ranar Litinin 14 ga watan Satamba 2020.