Coronavirus: Almajirai daga Kano ne su kara yawan masu cutar a Kaduna – Gwamna Elrufa’i

Gwamnan jahar Kaduna Nasir Elrufa’i ya ce sun samu karin mutum 19 masu dauke da Coronavirus, wanda hakkan ne ya  kara yawan masu cutar a jahar daga 9 zuwa 25.

Elrufa’i  ya wallafa hakkan ne a  shafinsa na Twitter, inda  ya ce an yi wa almajiran guda 40 gwaji, wanda  sakamakon  mutane 19 daga cikinsu ya nuna suna dauke da Coronavirus.

Gwamna Elrufa’i ya kuma kara da cewa yanzu ta tabbata shigi da fici da ake yi wa jahar tasa ne ke janyo karuwa masu cutar a Kaduna, inda ya ja hankalin jami’an tsaro da su ci gaba da sanya ido kan duk masu shiga birnin ta barauniyar hanya.

Ko a makon da ya gabata ma sai da gwamnan ya sanar cewa sun samu biyar daga cikin almajiran da aka mayar wa jahar tasa daga Kano masu dauke da cutar.

A kokarin dakile yadiwar cutar Covid19  a birnin Kano ne dai ya sa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya fito da shirin mayar da almajirai jahohinsu na asali.

Da dama masana harkar lafiya sun soki shirin bisa dogaro da cewa hakan ka iya yaduwar cutar a wasu jahohin da ba su da ita.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More