Coronavirus: An dakatar da gwajin rigakafi cutar a fadin Duniya

An dakatar da gwajin rigakafin cutar coronavirus a kan mutane a fadin duniya baki daya, bayan da wani mutum daga cikin wadanda suka yi kasadar mika kansu don gwajin rigakafin a Birtaniya ya kamu da tsananin rashin lafiya, wanda da ake ganin kila yana da alaka da allurar.

Wannan shi ne karo na biyu da aka dakatar da ci gaba da gwajin rigakafin, wanda jami’ar Oxford da ke Birtaniya da hadin gwiwar kamfanin samar da magunguna na AstraZeneca ke kokarin samarwa.

Mai magana da yawun kamfanin AstraZeneca ya ce an kwantar da mutumin a asibiti, kuma za a gudanar da wani bincike mai zaman kansa.

Sama da mutun dubu goma ne a kasashen Birtaniya da Brazil da Amurka da kuma Afrika ta kudu aka yi wa gwajin rigakafin.

Akwai rigakafin cutar Covid19 daban-daban har 30 ake gwajinsu a fadin duniya.

Sai dai na jamiar ta Oxford shi ne aka fi gamsuwa da ingancinsa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More