Coronavirus: An rufe Masallacin Annabi SAW dake garin Makkah

Hukumomi  kasar  Saudiyya sun bayar da umarnin rufe Masallacin Annabi (SAW) da ke Madina da kuma na Harami da ke Makkah saboda fargabar ci gaba da yaduwar coronavirus wacce aka sauya mata suna da Covid 19.

Sanarwar da hukumomin kasar suka fitar ta ce za a rufe dukkan hanyoyin da ke kai wa zuwa ga masallatan guda 2.

Hukumomin kasar sun ce liman ne kawai za a bari ya yi sallah tare da wasu tsirarun mutane.

Sai dai sun ce ba za a yi sallar Juma’a a masallatan ba.

Ma’aikatar lafiyar kasar ta sanar da cewa mutane 274 a yanzu suka kamu da cutar.

Da ma dai tuni aka hana masu zuwa Umrah da aikin Hajji shiga kasar, a wani mataki na hana ci gaba da yaduwar coronavirus wacce aka sauya zuwa Covid 19.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More