
Coronavirus: An samu karin mutune 58 da cutar a kasar Najeriya
An samun karin sabbin mutane 58 da suka kamu da cutar ta Covid19 a kasar Najeriya, wanda hakkan ne ya bada jumullar 59,345 da ke dauke da kwayar cutar.
Sabbin wayanda suka kamun sune:
Plateau-18
Lagos-15
Katsina-10
Ogun-5
Kaduna-4
Edo-3
Ekiti-1
FCT-1
Ondo-1
An sallami mutane 50,768 da suka warke daga cutar, inda hukumar NCDC ta tabbatar da mutuwar mutane 1,113 daga ranar Lahadi 28 ga watan satamba 2020.