Coronavirus: An tsawaita dokar hana fita a Kano na makonni biyu

Kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar Coronavirus ta sanar da cewa, an tsawaita dokar hana fita a Kano na makonin biyu bayan da wa’adin dokar ya kare a yau Litinin 18 ga watan Mayu 2020.

Shugaban kwamitin yaki da da Covid 19 ta fadar shugaban kasa,kuma sakataren gwamnati, Boss Mustapha, ya bayyana hakkan ne a wajen wani taron manema labarai na kullum kan matakan dakile Coronavirus a yau Litinin a birnin Abuja.

Haka kuma matakan bada tazara a tsakanin al’umma da aka dauka da suka hada da zirga-zirga tsakanin jahohi an tsawaita su, suma na makonni biyu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More