Coronavirus: Ana zargin mutane 27 da cutar a jahar Neja

Gwamnatin jahar Neja ta killace mutane 27 sakamakon   zargesu da ake yi na yin  mu’amala da wani mutum wanda ke dauke da kwayar cutar ta  coronavirus wacce aka sauya mata suna da Covid 19.

Mazauna kauyen Makira da ke jahar ne suka sanar da afkuwar lamarin ga hukumomi,  bisa nuna alamun cutar  da mutumin yayi.

Bayan zuwansu kauyen, don daukar mai dauke da cutar,yayi yukunrin barin kauye wajen bin motar kasuwa wanda ke dauke da wasu fasinjoji guda 26.

Sai dai  kwamitin ta jahar,sun gaggauta isa kauyen kuma sun samu nasarar kamashi a lokacin da yake kokarin tserewar.

Kwamishinan lafiya na jahar,dakta Mohammed Makusidi ya bayyana cewa an dauki jininsu kuma an kai Abuja don gudanar gwaji.

Yayin da kuma  suke killace a cibiyar killace masu dauke da cututtuka masu yaduwa na jahar ta Minna.

Inda kuma gwamnatin jahar za ta tabbatar da cewa an dauki dawainiyar ta hanyar da ta dace.

Channel ta rawaito cewa, mutumin  da ake zargin,  daga karamar hukumar Mashegu dake  jahar Legas yake.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More