Coronavirus: Ba’a kai lokacin da shugaba Buhari zaiyi bayani ba-Lai Muhammed

Lokaci bai yi ba da shugaban kasa Najeriya Muhammadu Buhari zai yiwa al’ummar Najeriya bayani a kan annobar coronavirus wacce aka sauya mata suna zuwa Covid 19. Inji ministan yada labarai na kasa wato Lai Muhammed.

Ministan labaran ya bayyana cewar, shugaba Buhari zaiyi bayani idan lokacin yayi, kuma a lokacin da ya dace.Anawa tunanina abinda ake son ji daga bakin shugaban kasar, shine ake ji daga gurinmu.

A karshe ya kara da cewa hakkan baya nuna cewa suna kare shugaba Buhari, domin akwai tabbacin cewa zai yi duk abunda ya dace dan ganin a samu cigaba mai kyau.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More