Coronavirus: Dalilin da yasa gwamnatin Kano ta tsawaita dokar hana fita na mako daya a jahar

Gwamnatin Jahar Kano ta sanar da tsawaita dokar hana a jahar ta mako daya a yunkurin ta na cigaba da hana yaduwar  annobar cutar ta  COVID-19.

Kwamishinan labarai na jahar, Muhammad Garba,  ne fitar da sanarwar cewa, an dauki matakin ne bayan tattaunawa da gwamnatin tarayya da masu ruwa da tsaki a fanin lafiya.

Ya ce an dauki matakin ne domin rage yaduwar cutar tsakanin mutane ta hanyar cudanya wadda ke daya daga cikin hanyar da cutar ke yaduwa kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Sanarwar ta yi kira ga alummar jahar su kara hakuri tare da ba wa gwamnati goyon bayan a yakin da ta ke yi da annobar duk da irin halin da mutane ke ciki ko suka tsinci kansu.

Ta kuma yi kira ga mutane su cigaba da tsafta ta hanyar yawaita wanke hannun su da sabulu, saka takunkumin fuska da kauracewa taron jama’a.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More